Yadda zaka gane idan mace tana S()nka ko.....
YADDA ZAKA GANE MACE NA SONKA
copied from.sadia abdu rano
Hikimomin Gane Idan Ana Sonka
Idan kana son ka gane da gaske ana
sonka, wadannan sune alamomin.
Wannan rubutu yana da dangantaka
ne da duk wanda yake tantamar
soyayyar da ake masa, ta haka ne zai
gane, duk da cewa dai soyayya ta
gaskiya ba a gane ta a lokaci kankani
kasancewar tana shiga ne sannu a
hankali. Ita soyayyar gaskiya tana
toho ne da yaduwa a cikin zukatan
mutane a yayin da ake zama ana
fahimtar juna. Wani abin bakin cikin
yanzu shine soyayyar gaskiya ba ta
cika dorewa ba. Wani lokacin sai an yi
nisa sai a ~ata ko ta lalace, Wannan
bayani ya gudana ne ga duk wani
masoyi da yake shakkun masoyiyarsa
ko tana son sa ko ba ta son sa.
• Idan tana yawaita fada maka tana
sonka kuma ka tabbatar da hakan,
tana jin son sosai a zuciyarta, sannan
kuma tana jin son ba tare da tana
rokonka wani abu ba, sakamakon
hakan ba ta jin bacin rai kuma ba ta
bata maka rai.
• Idan tana magana ka rinka kula da
idonta, wajen magana za ka iya gane
mace in tana sonka idonta yana nuna
alamun tausayi da soyayya ga wanda
take so da kauna. Duk ta kwayar
idonta za ka iya gane mace in
mayaudariya ce ko dabara da wayo
take maka. Shi ya sa aka ce abu mafi
sauki da muhimmanci ka rinka kula
da kwayar idonta wajen fahimtar son
da take maka in dai tana matukar
sonka za ka gani.
• Za ta rinka yin duk wani abu da ta
san zai faranta maka rai. Mata suna
nuna kulawa sosai ga wanda suka
damu da shi, shine sai a yi maka abu
ba tare da ka tambaya ba ko Ka nuna
kana so ba, in dai an san ka damu da
abin saboda son da ake maka. Za a yi
don a faranta maka rai. Wannan duk
alama ce ta ana sonka.
• In tana sonka babu ruwanta da
wasu samarin, na san ba kowane zai
yarda da haka ba. Amma soyayya ta
gaskiya ido rufewa yake, in dai mace
tana sonka idonta rufewa yake ba ta
ganin kowa a gabanta sai kai. Kar ma
ka damu kanka a kan da namiji
saboda idan idon sun rufe babu kowa
da ya mamaye zuciyar sai kai. To ka
ga kenan tunaninta, jinta da ganinta
duk naka ne.
• In tana matukar sonka za ta yi
kokarin ta ga ta magance duk wata
damuwa da ta shafe ka, da duk
matsalar da ta dame ka za ta rinka jin
duk wata damuwa taka kamar tata.
Saboda haka idan dai har mace tana
daukar damuwar wanda take tare da
shi kamar yadda za ta dauki tata
damuwar to a gaskiya wannan ita ma
alama ce ta tana sonka kuma tana
tare da kai.
• In tana sonka za ta rinka tinkaho da
alfahari da samunka, da kuma nunaka
a gurin ’yan’uwa da abokan arziki,
kawaye da sauran su. Saboda in mace
tana sonka gani take ka zama wani
bangare na jikinta. Wannan nem zai sa
ta rinka tinkaho da kai ba tare da jin
nauyi ko kunya ba.
• In tana sonka za ta rinka fifitaka a
kan ko wane abu, idan ma tana tare
da wasu da suke tare da ita ka shigo
kuma ta ji ta fi sonka to za ta fi fifitaka
a kansu kuma za ka gane, saboda za
ta fi son ta ga tana tare da kai ba tare
da gajiyawa ba, da son yin waya da
kai ba gajiyawa, sannan za ta rinka
goya maka baya da nuna maka
soyayya a kan za ta iya rabuwa da
kowa saboda kai.
• Damuwa da kulawa da kai a duk
lokacin da take tare da kai, mata suna
son su rinka kula da wanda suke
masa son gaskiya a cikin dadi ko
rashin dadi, ko da lafiya ko babu
lafiya kuma ba tare da nuna damuwa
ko bacin rai ba. Wadannan alamomi
sun isa su nuna maka mace tana sonka


Comments
Post a Comment